Gwamnatin na yaudarar ƴan Najeriya a kan yajin aiki–Kungiyar Likitoci
Kungiyar Likitocin Gwamnati Masu Neman Kwarewa (NARD) ta ce ikirarin Ma’aikatar Kwadago cewa an cika 19 daga cikin bukatun kungiyar 20 ba gaskiya ba ne, kuma gwamnati na kokarin yaudarar jama’a.
A cewar NARD, ba wani ainihin buƙatar da aka cika ko aka tabbatar an aiwatar.
Kungiyar ta ce mambobin ta ba su ga karin albashi ko alawus-alawus da ake cewa an fara biyan su ba. Haka kuma matsalolin basussuka, alawus ragowa da batutuwan rashin ma’aikata sun ci gaba ba tare da wani mataki na gaske ba.
NARD ta yi watsi da kafa sabbin kwamitoci, tana mai cewa abin da take nema shi ne:
Mayar da likitoci biyar da aka kora a FTH Lokoja da biyan su cikakkiyar diyya.
Biyan dukkan kuɗaɗen alawus na 2024.
Aiwatar da tsarin daukar likita sabo idan daya ya bar aiki.
Warware sauran matsalolin walwala da albashi.
NARD ta jaddada cewa yajin aikin da ta fara a ranar 1 ga Nuwamba, 2025 zai ci gaba har sai an cika wadannan bukatu, tana mai cewa lafiyar al’umma na cikin hadari saboda rashin aiwatar da alkawuran gwamnati.


