Ƴan bindiga sun bayyana kuɗin da za’a basu kafin sakin kiristocin da suka sace a jihar Kwara

0
6

’Yan bindigar da suka sace mutum kusan 35 daga cocin CAC a Eruku, a Jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 ga kowane mutum ɗaya a matsayin kuɗin fansa. 

Iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar cewa masu garkuwa suna amfani da wayar wadanda suka sace wajen kiran dangin su domin neman kuɗin.

Sakataren cocin ya ce an raba mutanen gida-gida, kuma rukuni na farko na mutum 11 aka fara nema. 

Wani tsoho mai suna Olukotun, ya ce shi ya tsira, amma mutane huɗu daga gidansa suna hannun ’yan bindigar.

Sarkin Eruku ya roki gwamnati ta gaggauta ceto mutanen, yayin da rundunar ’yan sandan jihar ta ce bata samu rahoton neman kuɗin fansa kai tsaye ba tukuna, amma jami’ai tare da sojoji na ci gaba da aikin ceto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here