Ƴan ta’adda tsagin Turji sun kai wa wasu ƙauyukan Sokoto mummunan hari

0
25

Wasu yan bindiga da ake zargin suna ƙarƙashin jagorancin sanannen ɗan bindiga Bello Turji, sun kai mummunan hari a kauyen Kurawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, dake Jihar Sokoto,  daren ranar Laraba.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu tare da sace mutane goma sha ɗaya.

Wani mai bayar rahoto kan rikice-rikice a arewa maso yamma, mai laƙabin Bakatsine, ya bayyana lamarin a wani saƙo da ya wallafa a X a ranar Alhamis.

Mazauna yankin sun ce yawan hare-haren ya jawo tsananin tsoro da durkushewar rayuwa, musamman a kauyukan da ke kan iyaka, inda da yawa daga cikinsu suka yin ƙaura saboda barazanar ’yan bindiga.

Har yanzu hukumomi ba su sanar da wani ci gaba a kan wannan lamari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here