Tinubu ya dakatar da tafiya Afrika ta Kudu da Angola saboda matsalolin tsaro

0
11

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu da kuma Luanda a Angola, domin samun cikakkun rahotannin tsaro kan sace ’yan makarantar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada na Cocin Christ Apostolic a Eruku, jihar Kwara.

Biyo bayan bukatar Gwamnan Kwara, shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tura karin jami’an tsaro zuwa Eruku da dukkan yankin karamar hukumar Ekiti, tare da umartar rundunar ’yan sanda da su bi diddigin maharan da suka kai wa mabiyan cocin hari.

Shugaban kasar dai ya shirya tafiya ne a yau daga Abuja domin halartar taron shugabannin G20 karo na 20 a kasar Afrika ta Kudu, sannan daga nan ya tafi Luanda don halartar taron koli na AU-EU karo na 7.

Sai dai matsalolin tsaro da suka kunno kai daga harin da ya rutsa da masu ibada a Kwara zuwa sace dalibai 24 a KebbI sun sa Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen tafiyar.

Yanzu haka shugaban kasar na jiran cikakken bayani daga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya ziyarci Kebbi domin jajantawa a madadinsa, da kuma rahotanni daga ’yan sanda da hukumar DSS game da harin da aka kai a Kwara.

Tinubu ya jaddada umarninsa ga jami’an tsaro da su tabbatar sun ceto daliban mata 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, tare da dawo da su gida cikin koshin lafiya.

A cewar Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, shugaban kasa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an shawo kan wadannan matsalolin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here