Nicki Minaj ta tabbatar da cewa ana yiwa kiristoci kisan gilla a Najeriya

0
6

Shahararriya mawaƙiya yar Amurka, Nicki Minaj, ta mara baya ga ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana cin zarafi tare da hallaka Kiristoci a Najeriya, zargin da gwamnatin Najeriya ta ƙarya ta.

Minaj, wadda ta halarci wani taro a birnin New York ranar Talata karkashin jagorancin Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Mike Waltz, ta bayyana godiyar ta ga Trump bisa yadda ya dage wajen jan hankalin duniya kan batun.

Idan za’a iya tunawa dai shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar kai hari Najeriya, in har gwamnati ta gaza kare kisan gilla da yace ana yiwa kiristoci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here