Sanata Garba Maidoki na Kebbi ta Kudu ya bayyana cewa an gano inda ’yan matan makarantar GGC Maga da aka sace suke, kuma ba a fitar da su daga yankin Kebbi ta Kudu ba.
Yayin tattaunawa da kafar talabijin ta Channels, a yau Laraba, sanatan ya ce akwai ƙwarin gwiwa cewa za a ceto ɗaliban cikin kwana ɗaya ko biyu.
’Yan bindiga sun kai hari makarantar a ranar Litinin, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar sannan suka tafi da dalibai kusan 25. Lamarin ya tayar da hankula a fadin ƙasa.
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin gaggawa ga jami’an tsaro su kubutar da su. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ziyarci yankin, inda ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don ganin an dawo da yaran lafiya.
Asusun UNICEF da sauran kungiyoyin duniya sun bukaci matakin gaggawa, akan lamarin yayin da Shugaba Tinubu ya dage wasu tafiye-tafiyensa saboda haka.
Harin ya sake jaddada matsalar garkuwa da ɗalibai a Najeriya, wadda ta dade tana faruwa tun bayan sace ’yan matan Chibok a 2014.


