Wata mummunar gobara da ake dangantawa da konewar maganin sauro ta kashe iyalai huɗu ’yan gida ɗaya a yankin Kundila, Layin Baba Impossible, cikin ƙaramar hukumar Tarauni a Kano, da misalin ƙarfe 4:13 na safiyar Laraba.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumar ta samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin ma’aikatan ta, HFS Abba Datti, a kan faruwar lamarin.
A cewar hukumar, ginin benen da mutanen suke ciki ya kama da wuta gaba ɗaya kafin zuwan jami’an kashe gobara.
Lamarin ya faru ga mutane 5 da suka haɗa da;
Hukumar ta tabbatar da rasuwar uwa da uba dake gidan tare da kananan ’ya’yansu biyu, yayin da Aminu, ɗan shekara 12, ya tsira da ransa.
Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga kunna maganin sauro da aka bari yana ci a rumfa yayin da iyalin suka yi bacci.


