Kotu ta janye belin waɗanda suka cire wa mace hanci a jihar Kano

0
17

Wata kotun majistare dake titin Zungeru a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Huda Haruna, ta soke bayar da belin wasu ’yan gida ɗaya da ake zargi da cire hancin makociyarsu bayan lakada mata duka a unguwar Rijiyar Lemo.

Lamarin ya faru ne lokacin da Rahama wadda ita ce mai kara ta je gidan Hassana Usman domin karɓar kuɗin da ta ba ta aro. 

A cewar bayanan kotu, ana zargin Hassana Usman tare da Umar Usman sun yi mata dukan kawo wuka, wanda ya janyo mummunar illa har ya kai ga cire mata hanci.

Tun da farko an gurfanar da su a kotun majistare ta Hajj Camp, inda aka ba su beli, amma an mayar da shari’ar zuwa kotun Zungeru bayan masu gabatar da kara sun koka kan yadda shari’ar ke tafiya.

Rahama ta samu munanan raunuka, inda aka garzaya da ita Asibitin Kashi na Dala, aka kuma yi mata aikin dasa hanci saboda tsananin lalurar da ta samu.

A zamanta na baya-bayan nan, Mai Shari’a Huda Haruna ta soke belin wadanda ake tuhuma, tare da umartar a tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 27/11/2025, lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’ar. Ta kuma umarci jami’an shari’a da su duba halin da mai kara ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here