Gwamnan Legas zai gabatar da kasafin kuɗin da ya zarce Naira triliyan 4

0
12

Gwamnatin Jihar Legas, karkashin jagorancin  Gwamna Babajide Sanwo-Olu, na shirin gabatar da sabon kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda darajar sa ta kai sama da naira tiriliyan 4.2.

A wata takarda da gwamnan ya mika wa Majalisar Dokokin Jihar, ya nemi ‘yan majalisar su ware masa wani lokaci domin ya bayyana cikakken tsare-tsaren kuɗaɗen shekara mai zuwa da gwamnatin sa zata aiwatar.

Sabon kudirin kasafin, wanda ya fi na bara yawa ƙwarai, ya haura kasafin 2025 da ya kai kusan naira tiriliyan 3.3. Wannan na nuna yadda kudaden gudanar da jihar ke ta ƙaruwa a kowace shekara.

Hakan kuma ya zama karo na biyar a jere da Legas ke fitowa da kasafi da ya wuce Naira tiriliyan ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here