Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana alhini kan kisan Brig. Janar M. Uba da mayakan ISWAP suka yi a Borno bayan yi wa rundunar sojoji kwanton ɓauna a kan hanyar Damboa, Wajiroko.
A cikin sakon da ya wallafa a X, Atiku ya zargi Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen kare rayukan ‘yan ƙasa, yana mai cewa gwamnatin ta fi maida hankali kan danniya ga ‘yan adawa maimakon tsaro.
Ya ce idan shi ne shugaban ƙasa, da ya umarci dakarun soja su mamaye Borno ko kowace jiha da ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda suka addaba, har sai an kawar da barazanar tsaro daga cikin su.
Atiku ya kuma zargi rundunar soji da rashin fitar da sahihin bayanai kan lamarin, yana mai cewa kisan Janar Musa da sojojin da ke ƙarƙashinsa “abun takaici ne kuma ya nuna tashin hankali na ‘yan ta’adda yana ƙara kamari”.
Ya ja hankalin gwamnati cewa tsaron rayukan ‘yan ƙasa shi ne jagorancin da ya fi muhimmanci, yana mai kira ga shugabanni da al’umma su kasance da fatan cewa wannan yanayi zai shuɗe.


