Majalisar wakilai ta rage yawan shekarun tsayawa takarar gwamna da sanata

0
29

Majalisar Wakilai ta amince da wani kudirin gyaran kundin tsarin mulki a karatu na biyu, wanda ke neman rage shekarun da ake bukata mutum ya kai domin tsayawa takarar gwamna da sanata daga 35 zuwa 30.

Kudirin, wanda aka yiwa laƙabi da HB. 2235, ya samu goyon bayan ɗan majalisa Esin Etim tare da wasu ‘yan majalisa 24. A tsarin yanzu, ana bukatar mutum ya kai akalla shekara 35 kafin ya iya shiga takarar gwamna ko sanata, yayin da kujerar Majalisar Wakilai ke bude ga wadanda suka kai shekara 25.

Etim, wanda ke wakiltar Offong/Oruko/Udung Uko a jihar Akwa Ibom, ya ce tsarin yanzu yana tauye damar ci gaban matasa a siyasa, musamman wadanda suka fara tafiyar siyasa tun suna ƙuruciya. 

Bayan gabatar da kudirin, Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya yi amfani da kuri’ar murya domin kada kuri’a, inda mafi yawan ‘yan majalisa suka goyi bayan kudirin ba tare da muhawara ba.

An kuma tura kudirin zuwa ga kwamitin duba kundin tsarin mulki domin ci gaba da tantancewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here