Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja
Jami’an tsaro sun mamaye hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wuse Zone 5, Abuja, kafin gudanar da taruka biyu daban-daban da bangarorin jam’iyyar ke shirin yi.
Manema labarai sun hango aƙalla motoci 15 kirar Hilux da manyan motocin sulke guda biyu a gaban ofishin.
’Yan sanda da jami’an Civil Defence sun bazu a muhimman wuraren dake kusa da sakatariyar jam’iyyar.
A ranar Litinin, sabon shugaban jam’iyyar da bangaren sa ya zaɓi, Barista Tanimu Turaki (SAN), ya ce ya nemi kariyar ’yan sanda domin gudanar da zaman farko na sabon Shugabancin da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar. Ya ce bangaren Abdulrahman Muhammed da ake dangantawa da Ministan FCT, Nyesom Wike, ba wakilan PDP ba ne.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, ba a ga ko wane bangare ya isa hedikwatar jam’iyyar ba.


