Dole ne a Kawo ƙarshen cin hanci a harkokin shari’a—Tinubu

0
9

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci alkalan Najeriya da su kare mutuncin shari’a, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya ba za ta tsayu ba, ba tare da adalci ba. 

A wani taron shekara-shekara na alkalan Najeriya, Tinubu ya ce dole kotuna su nisanci cin hanci da duk wani tasiri na siyasa, domin rashin adalci na rusa kasa gaba ɗaya.

Masana, ciki har da Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, sun nuna damuwa kan yawan hukunce-hukuncen da ke karo da juna da kuma tsoron da wasu alkalai ke yi na yanke hukunci idan gwamnati ta shigo ciki. 

Ya zargi ’yan siyasa da katsalandan a shari’a, yana mai misali da rikicin cikin jam’iyyar PDP, inda kotuna daban-daban ke bayar da sabanin hukunci.

Farfesan ya ce kiran Tinubu ba shi kaɗai zai isa ba, yana neman a ladabtar da alkalan da ke karya ƙa’ida, tare da ɗaukar tsauraran matakai don tabbatar da cewa an naɗa alkalan da suka cancanta, masu gaskiya da tsoron Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here