Dole a yi amfani da ƙwarewa wajen ceto ɗalibai mata a jihar Kebbi–Waidi

0
5

Shugaban Rundunar Sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun Operation FANSAN YANMA da su ƙara ƙaimi wajen kubutar da daliban makarantar sakandiren ƴan mata ta Maga, da aka sace a karamar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.

Janar Shaibu ya ba da wannan umarni ne a ranar, 17 ga Nuwamba 2025, yayin ziyarar aikin da ya kai jihar. 

Yayin jawabi ga kwamandoji da dakarun da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar ya bukaci su gudanar da ayyukan leken asiri da kuma bin sawun ‘yan bindigar ba dare ba rana, tare da amfani da dukkan bayanan sirri da suka samu. “Dole ne mu nemo waɗannan yara. Ku yi aiki da ƙwarewa da gaggawa. Ba mu da zaɓin gazawa,” in ji shi.

COAS ɗin ya kuma gana da jami’an sa-kai da mafarauta, inda ya bayyana su a matsayin muhimman abokan aiki. Ya bukace su su yi amfani da sanin da suke da shi kan dazukan yankin tare da haɗin gwiwar sojoji domin gano maboyar ƴan ta’adda.

A yayin ziyarar, Janar Shaibu ya jajanta wa Sarkin Danko, Alhaji Abubakar Ibrahim Allaje, da kuma shugabar makarantar GGCSS Maga, Hajiya Rabi Musa Magaji, inda ya tabbatar musu da cewa rundunar soja za ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto daliban lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here