Al’ummar yankin Jajira dake ƙaramar hukumar Ungogo, sun roƙi gwamnati ta buɗe musu hanyar da aka rufe a yankin sakamakon aikin shimfida layin dogo da ya biyo ta garin.
Daily News 24 Hausa, ta rawaito cewa, wasu daga cikin al’ummar Jajira da suka zanta da manema labarai, sun bayyana cewa rufe titin nasu ya jefa su cikin kunci da koma bayan tattalin arzikin su maimakon samun cigaba.
Sun ƙara da cewa sun tuntubi kamfanin da yake yin aikin don buɗe hanyar amma yace ce sai gwamnan jihar Kano ya saka baki ko ministan sufuri sannan za’a bude hanyar, saboda akwai wasu kuɗaɗen da ya kamata a biya kamfanin domin gina gadar da zata bawa al’umma damar yin zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
Mutanen sun roƙi gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa a sake buɗe titin Jajira.


