Ma’aikatan fannin lantarki zasu katse wutar lantarkin Najeriya

0
13
wutar lantarki

Ma’aikatan fannin lantarki zasu katse  wutar lantarkin Najeriya

Ƙungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi barazanar katse wutar lantarki a fadin ƙasar nan, bayan zargin cewa an kai wa ma’aikatan Kamfanin Rarraba Lantarki hari a Jihar Imo.

A wata sanarwa da mukaddashin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike, ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ’yan sanda da ake zargin sun kai hari a cibiyar lantarki ta Egbu da ke Owerri. Rahoton ya ce jami’an sun doki ma’aikata, sun tsoratar da su da bindigogi, har ma suka kama wasu daga cikinsu.

Har ila yau, an ce ’yan sandan sun lalata wasu kayayyakin aikin ma’aikatan tare da dakatar da ayyukan da ake gudanarwa, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

NUEE ta ce ta riga ta umarci mambobinta da su katse wutar lantarki a Jihar Imo har zuwa lokacin da za’a warware matsalar.

Ƙungiyar ta kuma gargadi cewa za ta iya tsayar da wuta a fadin Najeriya, sai dai idan hukumomi sun ɗauki matakan gaggawa don kare tsaron ma’aikatan lantarki a duk faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here