Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙwarai damuwarta kan sace ɗalibai mata daga makarantar sakandire ta Maga, dake ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati na tare da iyalan waɗanda aka sace, tare da tabbatar musu da cewa ana ƙoƙarin ganin an dawo da su cikin koshin lafiya.
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dage wajen kare rayukan ’yan Najeriya, musamman yara a yankunan da ke fama da barazanar tsaro.
Idris ya la’anci harin da ’yan bindiga suka kai, wanda ya haifar da mutuwar wasu jami’an makarantar, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba har sai an kamo wadanda suka aikata laifin an gurfanar da su tare da fuskantar hukunci.


