A ranar Lahadi wani jami’in Rundunar Sojojin Ruwa, Lt. A.M. Yarima, ya tsira daga abin da ake zargin yunkurin kisan gilla a Abuja, in ji majiyoyin tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ba, sanye da bakaken kaya, a cikin motoci biyu kirar Hilux marasa lamba, sun bi diddigin Yarima daga tashar NIPCO kusa da Line Expressway zuwa Gado Nasco Way misalin ƙarfe 6:30 na yamma.
Majiyar ta ce jami’in ya lura da abin da ke faruwa, inda ya yi dabara ta musamman don kubuta daga cikin haɗarin. Ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma hukumomi sun takaita bayani domin kada ya shafi binciken.
Wannan al’amari ya faru ne ‘yan kwanaki bayan tirka-tirkar da ta barke tsakanin Yarima da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a wani yankin filin da ake gardama a Gaduwa. Bidiyon fadan ya yadu sosai, lamarin da ya sa aka dakatar da rusau a wurin.


