Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, John Bonzena, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, kwanaki biyu kafin gwamna Agbu Kefas ya bayyana sauyin jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar mai mulki.
A wannan sauyi, ɗaukacin manyan jami’ai da sauran ‘yan majalisar da ke PDP sun bi sahun Bonzena zuwa APC.
Faifan bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna ƴan majalisar suna cire hulunan alamar jam’iyyar PDP tare da sanya hulunan da ke dauke da tambarin Shugaba Bola Tinubu, tare da rike tsuntsiya.
Idan za’a iya tunawa a ranar Asabar da ta gabata Gwamna Kefas ya tabbatar da cewa zai bar PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin “ya shafi makomar al’ummar Taraba”.


