Dan gwagwarmaya Omoloye Sowore, ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta saki malamin addini Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, yana mai cewa cigaba da tsare shi “cin zarafin ra’ayin addini ne.”
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Lahadi, Sowore ya bayyana cewa ya shirya ziyarar ganawa da Sheikh Abduljabbar a gidan yari, sai dai yanayin da ya ji ake tsare da shi ya tayar masa da hankali.
Ya rubuta cewa: “Abin takaici ne kuma babu adalci a rike wani malamin addini saboda kawai fahimtarsa ko tafsirin sa bai yi daidai da wanda masu mulki ke so ba.”
Daily News 24 Hausa, ta tuna cewa a ranar 15 ga Disamba, 2022, Babbar Kotun Shari’ar Muslunci ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola, ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin sabatanci ga Manzon Allah (SAW).
Gwamnatin Kano ta gurfanar da malamin bisa zargin yin furucin batanci a lokuta daban-daban a shekarar 2019.
Sowore ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta daina danniya ga masu sabanin ra’ayin addini, yana mai kira ga hukumomin tarayya da kungiyoyin kare haƙƙin mutane su shiga cikin lamarin.


