Nnamdi Kanu na neman diyyar Naira biliyan 50 a wajen likitocin Najeriya

0
7

Shugaban ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra IPOB Nnamdi Kanu, ya maka Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA) a kotu yana neman diyyar Naira biliyan 50, yana zargin cewa sun fitar da rahoton ƙarya akan lafiyar sa, da ya bayyana cewar yana da cikakkiyar lafiyar fuskantar shari’a.

Kotun tarayya ce ta bai wa NMA umarni su binciki lafiyarsa, amma Kanu ya ce babu wani likita daga kwamitin da ya ziyarce shi ko ya duba shi. Duk da haka, kwamitin ya gabatar da rahoto cewa yana da ƙoshin lafiya.

Kanu ya ce rahoton da aka fitar dangane da lafiyar sa na bogi ne, an yi shi ba tare da gwaji ba, kuma hakan yaudarar kotu ne, ya kuma hana shi samun magani ko belin da yake nema. Ya bayyana cewa hakan ya janyo masa matsanancin ciwo da tauye masa haƙƙin ɗan Adam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here