Nayi sanadiyyar yin sulhu da ƴan ta’adda 600–Sheikh Ahmad Gumi

0
10

Shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya mayar da martani kan masu cewa a kama shi saboda tsokacinsa game da batun ’yan bindiga da tsaro a ƙasar nan.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, Gumi ya zargi masu sukar sa da rashin gaskiya da son zuciya, yana mai cewa suna fifita hayaniya maimakon neman mafita.

Gumi ya tuna wani babban shiri na tattaunawa da ya jagoranta a Janairun 2021 a dajin Sabon Garin Yadi, Jihar Kaduna, inda shi tare da Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar a wancan lokaci suka gana da fiye da ’yan bindiga 600 da shugabanninsu. Ya ce a wannan taron, sun samu alƙawarin su ajiye makamai idan an ba su tsaro da wasu muhimman abubuwan more rayuwa.

Ya bayyana cewa gwamnati ba ta cika wa waɗannan mutane sharuɗɗan da suka gindaya ba, abin da ya kawo rushewar damar sulhu da kuma ci gaba da tashin hankali.

Malamin ya yi tambaya kan dalilin da yasa neman sulhu zai zama abin da zai haifar da kira da a kama shi, yana mai jaddada cewa yin magana cikin ’yanci wani haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya tanada.

Gumi ya bukaci ’yan Najeriya da su daina yin hukunci da zuciya, su kuma mai da hankali wajen samar da hanyoyin da za su rage rikice-rikice a ƙasar, maimakon kai farmaki ga waɗanda ke kokarin kawo mafita ta hanyar tattaunawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here