Kuka nake yi duk lokacin da naji labarin kashe mutane a Najeriya–Akpabio

0
10

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na da alhakin dawo da zaman lafiya a Jihar Plateau da kuma Najeriya gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa babu wata ƙasar waje da za ta zo ta samar wa Najeriya zaman lafiya idan ‘yan kasar ba su rungumi zaman tare ba.

Akpabio ya yi wannan bayani ne a ranar Asabar a filin Polo na Jos, yayin taron tarbar sabbin ‘yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a jihar.

Ya tabbatar wa al’ummar Plateau cewa Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar dakile rikice-rikice da kashe-kashe da suka addabi jihar da sauran sassan ƙasar.

> “Muna roƙon Allah ya taimake mu wajen dawo da zaman lafiya a Plateau. Wanda zai mulki wannan jiha dole ya zama mai kishin zaman lafiya. Mun isa mu kawo sauyi. Ba kasashen waje ne za su kawo mana zaman lafiya ba, mu da kanmu ne,” in ji shi.

Akpabio ya kara da cewa yana jin haushi da takaici, yana zubar da hawaye duk lokacin da ya ji labarin mutuwar mutane yara ko manya yana mai nuna damuwa da yadda zubar da jini ya yi yawa a Najeriya.

Ya ce matsalolin tsaro a Plateau ba sabon abu ba ne, domin tun kimanin 2010 rikice-rikice suka fara kamari, yana tunawa da irin rahotannin da aka fitar wancan lokacin.

Shugaban Majalisar Dattawan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya, tare da roƙon mutanen Plateau su mara wa Tinubu da APC baya domin ganin cigaba ya zo musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here