Mayakan ISWAP sun kai wa wasu dakarun sojin Najeriya hari a jihar Borno da yammacin ranar Juma’a, inda suka hallaka wasu sojoji tare da yin garkuwa da babban jami’in soja, kamar yadda rahoton HumAngle ya bayyana.
Jami’in da aka sace, wanda aka bayyana a matsayin kwamandan brigade, shi ne yake jagorantar tawagar lokacin harin. Idan wannan batu ya tabbata, zai kasance karo na farko da ƙungiyar masu ta’addanci ta kama babban jami’in soja mai aiki kai tsaye daga fagen daga a Najeriya.
Ko da yake an taɓa kashe manyan hafsoshin soja a hare-haren baya, kamawa ko garkuwa da su abu ne da ba kasafai yake faruwa ba. Harin ya kuma kashe wasu ‘yan sa-kai na CJTF.
Har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa game da lamarin ba. Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Onyechi Anele, bai amsa sakonnin neman bayani ba, kuma ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.


