Fintiri ya nesanta kansa da hukuncin korar Wike daga PDP

0
6

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana adawarsa ga matakin da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka dauka na korar  Ministan Abuja (FCT), Nyesom Wike, daga jam’iyyar.

An kori Wike tare da tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, da Sanata Samuel Anyanwu a lokacin babban taron PDP da ake gudanarwa a Ibadan, bayan Bode George ya gabatar da kudurin korar su, kuma shugaban PDP na Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya.

Sai dai Fintiri a cikin wata sanarwa ya ce ba ya goyon bayan hukuncin da aka yanke, yana mai cewa hakan ba zai amfani jam’iyyar ba.

Fintiri ya jaddada bukatar sasanci da warware matsaloli, yana kira ga shugabanni da su mayar da hankali kan haɗa kan jam’iyya.

Ya kara da cewa burinsa shi ne ganin PDP ta samu zaman lafiya da ci gaba.

Fintiri na daga cikin gwamnoni huɗun da suka halarci taron, kuma shi ne shugaban kwamitin shirya taron.

Sai dai Gwamnonin Osun (Adeleke), Taraba (Kefas), da na Ribas (Fubara) ba su halarci taron ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here