’Yan bindigar da suka sace daraktoci 6 na ma’aikatar tsaro sun nemi maƙudan kuɗin fansa

0
18

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar da suka sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaro a kan titin Kabba–Lokoja, a jihar Kogi, sun nemi kudin fansa na Naira 150 miliyan.

’An yi garkuwa da su ne a ranar 10 ga Nuwamba, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Legas zuwa Abuja don zana wata jarabawar karin girma. 

Wasu rahotanni sun ce harin ya kasance shiri na musamman.

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya ce suna cikin tashin hankali, kuma ba su da ikon tara adadin kuɗin da ake nema. Ya roƙi ’yan bindigar da su saki iyalansu cikin koshin lafiya.

Kungiyar ma’aikatan ma’aikatar tsaro (ASCSN) ta tabbatar da sacewar, tana mai cewa an dauki matakai tare da jami’an tsaro don ceto daraktocin.

An bayyana sunayen waɗanda aka sace da Ngozi Ibeziakor, C. Emeribe, Helen Ezeakor, C. Ladoye, J. Onwuzurike, da Catherine Essien, dukkansu ma’aikatan Command Day Secondary School, Ojo, Legas.

Kungiyar ta tabbatar cewa ma’aikatar ta tura jami’an tsaro domin ganin an ceto su ba tare da lahani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here