Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya biyu FAO da WFP sun saka Najeriya cikin jerin ƙasashe 16 da suka fi fama da yunwa a duniya, inda matsalar tsaro ke ƙara dagula halin da mutane ke ciki.
Wani rahoto ya nuna cewa ƙasashe irin su Haiti, Mali, Falastin, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen suna cikin babbar barazanar bala’in yunwa, yayin da ƙasashe kamar Afghanistan, DR Congo, Myanmar, Najeriya, Somaliya da Syria ke buƙatar gaggawar tallafin abinci.
Haka kuma Burkina Faso, Chadi, Kenya da sansanonin Rohingya a Bangladesh na daga wuraren da damuwa kan yunwa ke ƙaruwa. Rahoton ya danganta matsalar da rikice-rikice da tashe-tashen hankula.
A cewar Aliyu Dawobe na Red Cross, sama da mutane miliyan 3.7 a arewa maso gabashin Najeriya na cikin matsanancin bukatar abinci, musamman yara, mata masu juna biyu da masu shayarwa. Y
Ya ce shekaru 15 na rikicin Boko Haram sun hana manoma yin noma, wanda ya kara tsananta ƙarancin abinci.
Rahoton ya gargadi cewa matsalar yunwa na iya ta’azzara idan ba a dauki matakin gaggawa ba.


