Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya zargi gwamnatin mulkin mallaka ta Biritaniya da cewa ita ce ta dasa tushen ƙabilanci da wariyar addini a Najeriya, abubuwan da har yanzu ke raba kan ‘yan ƙasa shekaru da dama bayan samun ‘yancin kai.
Da yake magana a shirin Morning Show na gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, George ya bayyana cewa waɗannan matsaloli biyu ne suke haddasa yawancin rikice-rikicen siyasa da na zamantakewa a ƙasar. Ya ce gazawar Najeriya wajen shawo kan son ƙabila da bambancin addini shi ne babban cikas ga ci gaban ƙasa.
Ya ce bambancin al’adu da addinai a Najeriya bai kamata ya zama abin raba jama’a ba, domin a baya, hulɗar addinai da ƙabilu ta kasance abin alfahari.
Jawabin Bode George ya zo ne yayin da ake ta tattaunawa kan zarge-zargen kisan Kiristoci a Najeriya da kuma gargadin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya ɗaukar mataki idan gwamnatin Najeriya ta kasa dakile hakan.
George ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji son ƙabilanci da rikicin addini, su mai da hankali wajen gina ƙasa ɗaya mai zaman lafiya da adalci.
> “Wannan batun ƙabila da addini ba shi da alaƙa da yadda ake tafiyar da ƙasa. Abin da muke bukata shi ne haɗin kai da gaskiya,” in ji shi.


