Majalisar wakilai ta nemi a dakatar da fara zana jarabawar WAEC a kwamfuta

0
13

Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin da hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta WAEC ke shirin aiwatarwa na amfani da kwamfuta a jarabawar shekarar 2026, tana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da gazawar dalibai da dama.

Wannan kiran ya biyo bayan wani kuduri da dan majalisa Kelechi Nworgu ya gabatar, inda ya bukaci majalisar ta shiga tsakani kan abin da ya bayyana a matsayin barazana ga ci gaban ilimi a Najeriya.

Nworgu ya bayyana cewa duk da ana gudanar da jarabawar JAMB ta hanyar kwamfuta, yanayin da yawancin makarantun sakandire ke ciki a Najeriya bai dace da irin wannan sauyi ba a halin yanzu.

A cewarsa, “Daga cikin makarantun sakandire sama da 25,500 da muke da su a fadin ƙasar nan, musamman a yankunan karkara, da yawa ba su da kwamfutoci masu aiki, ko kuma malamai da suka kware wajen koyar da ilimin kwamfuta. A gaskiya, wasu daliban ma ba su taɓa amfani da kwamfuta ba, amma yanzu ana son a tilasta musu zana jarabawa da ita.”

Dan majalisar ya bukaci ma’aikatar ilimi tare da hukumar WAEC su jinkirta fara amfani da kwamfuta a jarabawar na tsawon shekaru uku, domin a yi shirin da ya dace da kuma samar da kayan aiki da horo kafin aiwatar da tsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here