Jami’in EFCC ya sace wasu maƙudan kuɗaɗe

0
10

Kotun jihar Kaduna ta dage sauraron shari’ar tsohon jami’in Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Polycarp Andrew, zuwa ranar 11 ga Disamba, 2025.

Andrew, wanda tsohon mai kula da shaidu ne a ofishin EFCC na yankin Kaduna, ana tuhumarsa da aikata laifin karkatar da kudade da suka kai sama da Naira miliyan 22 da aka ajiye a hannunsa a matsayin shaida a tsakanin shekarun 2023 da 2024.

An gurfanar da shi a gaban kotu tun ranar 5 ga Mayu, 2025, bisa tuhuma guda shida da suka shafi cin amana. Sai dai musanta aikata laifin.

A zaman kotu na baya-bayan nan, lauyan EFCC, H.M. Mohammed, ya bayyana cewa hukumar ta shirya gabatar da shaidu biyu, daya daga cikin jami’an EFCC da kuma ma’aikacin kamfanin Opay. Sai dai lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, D.B. Kwajafa, ya nemi a dage shari’ar saboda yana bukatar karin lokaci domin nazarin bidiyon bayanin da wanda ake tuhuma ya yi wajen bincike.

Bayan sauraron bangarorin biyu, mai shari’a A. Bello ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 11 ga Disamba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa Andrew ya gudu zuwa jihar Taraba bayan zarginsa da karkatar da kudaden da aka ajiye a hannunsa. Kudaden sun hada da dala $11,900 (kimanin N10.9m), $3,800 (N5.9m), da $2,800 (N3.8m).

Laifin, a cewar EFCC, ya saba da sashe na 300 na dokar Penal Code ta jihar Kaduna ta 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here