Gwamnatin tarayya ta dakatar da sabon harajin man fetur da dizal
Hukumar kula da harkokin albarkatun man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta sanar da dakatar da karɓar harajin kashi 15% da aka shirya sakawa kan shigo da man fetur da dizal.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, inda Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya tabbatar da cewa ba za a aiwatar da harajin ba.
Tun da farko, rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan harajin na kashi 15% ga man fetur da dizal da ake shigo da su cikin ƙasa, amma hukumar ta bayyana cewa an jingine shirin.
NMDPRA ta ƙara da cewa, yanzu haka Najeriya na da isasshen adadin man fetur da zai iya biyan buƙatar yan ƙasa baki ɗaya, har ma a lokacin bukukuwan karshen shekara da ake amfani da mai mai yawa.
Hukumar ta shawarci ‘yan ƙasa da su guji sayan mai fiye da kima ko ɓoyewa, domin hakan na iya jawo ƙarancin mai da tashin farashi.


