Dangote ya zuba hannun jarin maƙudan kuɗaɗe a ƙasar Zimbabwe

0
36

Dangote ya zuba hannun jarin maƙudan kuɗaɗe a ƙasar Zimbabwe

Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, wanda shi ne attajirin da ya fi kowa yawan arziki a nahiyar Afrika, ya bayyana cewa kamfaninsa ya sanya hannu kan yarjejeniya da gwamnatin Zimbabwe domin zuba jarin sama da dala biliyan ɗaya ($1bn) a fannin siminti, makamashi, da bututun mai.

Dangote ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, a Harare babban birnin ƙasar a ranar Laraba. Ya ce yarjejeniyar ta haɗa da gina masana’antar siminti, tashar samar da wutar lantarki, da kuma bututun isar da mai daga kasashen waje zuwa cikin Zimbabwe.

Ya ƙara da cewa jarin zai haura dala biliyan ɗaya saboda girman aikin bututun mai, kuma akwai wasu ƙarin shirye-shiryen zuba jari da kamfaninsa ke duba yi a ƙasar.

Dangote, ya riga ya kaddamar da ayyuka makamantan haka a wasu ƙasashen Afrika, ciki har da Ethiopia da Zambiya. A watan Oktoba 2025, kamfanin ya fara gina masana’antar takin zamani ta kuɗi dala biliyan 2.5 a birnin Gode na Ethiopia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here