Ɗan majalisa mai wakiltar birnin Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

0
14

Dan majalisar tarayya mai wakiltar birnin Kano Hon. Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP.

A cikin wata wasiƙar da ya aikawa Shugaban jam’iyyar NNPP na mazabar sa ta Zaitawa a ranar 11 ga Nuwamba, 2025, Koki ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar saboda rikicin cikin gida da ke addabar shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Koki, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur, ya gode wa jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi ya yi aiki a ƙarƙashin ta, inda ya bayyana goyon baya da kwarewar da ya samu a matsayin “abin da ba za a manta da shi ba.”

Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba ko matakin da zai ɗauka nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here