Zanga-zangar rashin tsaro tayi sanadiyar mutuwar mutum a Katsina

0
10

Mazauna ƙauyukan Danjanku, Dantashi da Dayi a ƙaramar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, sun gudanar da zanga-zanga bayan sabon harin ‘yan bindiga da ya kashe mutum ɗaya tare da sace wasu 17.

Harin na Litinin da daddare shi ne na uku cikin mako guda, inda adadin mutanen da aka sace ya kai sama da 30.

Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Funtua–Katsina don nuna fushinsu kan yadda gwamnati ta kasa kawo ƙarshen hare-haren, amma lamarin ya rikide zuwa tashin hankali bayan jami’an tsaro sun zo tarwatsa su, inda aka kashe mutum ɗaya.

Daga bisani, shugabannin gargajiya sun shiga tsakani suka kwantar da tarzomar. Mazauna yankin sun koka cewa duk da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati ta kulla da ‘yan bindigar, har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare da karɓar haraji daga manoma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here