Babu gwamnan da zai yi kukan rashin kuɗi a mulkin Tinubu, inji gwamnan Legas

0
14

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai ce gwamnati na fama da ƙarancin kuɗi.

Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a Kaduna yayin wani taron bita na kwana ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya don tunawa da cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai.

Ya ce an samu ƙaruwa mai yawa a rabon kudaden gwamnatin tarayya, wanda hakan ya bai wa jihohi da ƙananan hukumomi damar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa.

A cewar gwamnan, daga 2023 zuwa 2024, rabon jihohi ya ƙaru da kashi 62%, yayin da na ƙananan hukumomi ya tashi da kashi 47%. 

Sanwo-Olu ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa tabbatar da ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi, wanda kotun koli ta tabbatar. Ya ce wannan ci gaba ne babba a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya ƙara da cewa mataki na gaba da shugaba Tinubu ke shirin ɗauka shi ne ƙirƙirar ’yan sandan jihohi, domin inganta tsaro a ƙasar nan.

A nasa jawabin, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Pius Anyim, ya ce tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a muhimmin abu ne don nasarar manufofin gwamnati.

Shi ma mai shirya taron, Muhammad Yakubu, ya nuna tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta kai Najeriya ga ci gaba, musamman a fannoni kamar ilimi, noma, da gine-gine.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here