Wani da ake zargin barawo ne ya shiga Gidan Gwamnatin Kano da asuba a ranar Litinin, inda ya yi awon gaba da wata motar Toyota Hilux dake cikin ayarin motocin dake rakiyar mataimakin gwamnan jihar.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru da kimanin ƙarfe 5 na safe, bayan wanda ake zargin ya samu damar shiga ta Kofa ta 4 dake gidan gwamnatin sannan ya fice ta babban ƙofa ba tare da an lura da shi ba.
Majiyoyi daga Gidan Gwamnatin sun tabbatar cewa hoton na’urar CCTV da aka duba ya nuna barawon yana tuƙa motar yayin da yake fita daga harabar gidan gwamnati.
Direban motar, wanda aka bayyana da suna Shafiu Sharp-Sharp, ya sha tambayoyi kuma aka tsare shi na ɗan lokaci domin bincike.
Majiyar jaridar Kano Times, ta rawaito cewa an kaddamar da bincike kan wannan lamari.
Jaridar tace kokarin samun mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, wato Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ci tura, domin bai ɗaga waya ba kuma bai amsa sakonni da aka tura masa ba.


