An rasa inda aka kai Naira triliyan 210 daga asusun NNPC–Majalisa

0
10

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa dole ne Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya mayar da kuɗaɗen da ba a bayyana yadda aka yi da su ba, waɗanda suka kai naira tiriliyan 210, zuwa Asusun Tarayya.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lissafin Kuɗaɗen gwamnati ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada ne ya yanke wannan hukunci, bayan shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ya gaza bayyana a zaman kwamitin domin ya fayyace amsoshin tambayoyi da aka aika masa ba.

A binciken da aka gudanar kan ayyukan NNPCL daga shekara ta 2017 zuwa 2023, kwamitin ya gano kuɗaɗe da ba a iya bayyana yadda aka yi da su ba da suka kai naira tiriliyan 103 a matsayin kuɗin kashewa da kuma naira tiriliyan 107 a matsayin abin da ake bin kamfanin bashi.

Sanata Wadada ya ce bayanan da kamfanin ya bayar suna cike da sabani da rashin daidaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here