Ƴan bindiga sun kai hari tare da sace mata a jihar Kano

0
14

’Yan bindiga sun kutsa kauyen Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono a Kano, inda suka yi garkuwa da mata biyar, ciki har da masu shayarwa.

Lamarin ya faru ne daren Lahadi kusan ƙarfe 11 na dare, lokacin da maharan suka dira garin Yan Kwada suna harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin kafin su yi awon-gaba da matan.

Wani mazaunin yankin ya ce ’yan bindigar sun ratsa gidaje suna  fass ƙofa da harbi kafin su tafi da wadanda suka sace. Daga baya mata biyu sun samu dawowa gida, yayin da uku har yanzu ke hannun masu garkuwa.

Hare-haren sun ƙara tayar da hankula a ƙauyukan Kano, musamman yankunan da ke iyaka da Katsina, inda ake zargin matsin lamba daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Katsina ke korar miyagun zuwa Kano.

Masana tsaro da shugabannin al’umma sun yi kira ga Gwamnatin Kano da ta inganta tsaro a yankunan kan iyaka tare da haɗa kai da gwamnatin Katsina domin dakile yada hare-haren.

Lamarin ya faru ne cikin mako guda bayan da sojoji suka kashe wasu ’yan bindiga 19 a yankin. Mutane da dama a Faruruwa da makotan kauyuka sun tsere zuwa birane domin neman tsira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here