Trump ya janyo mummunar asara ga kasuwar hannayen jari ta Najeriya 

0
10

Kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi rugujewar daraja cikin makon farko na Nuwamba, inda aka yi asarar Naira triliyan 2.8 saboda fargabar da ta biyo bayan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan yiyuwar farmakar Najeriya.

Daga ranar 3 zuwa 7 ga Nuwamba hannayen jari sun sauka sosai. A ranar farko bayan barazanar, an yi asarar Naira biliyan 244.9, sannan raguwar ta kai Naira biliyan 611.9, a Talata, Naira triliyan 1.31,  a Laraba, Naira biliyan 347.7, a Alhamis, da Naira biliyan 318.7, a Juma’a.

Bangarorin da suka fi fuskantar koma baya sun haɗa da bankuna, man fetur da kayan masarufi. Kamfanoni 75 ne suka yi mummunar asara a farashin hannunsu.

Haka kuma, kamfanin MTN Nigeria ya rasa 8.3% na darajar hannun jari.

Masana sun ce barazanar Trump ta tayar da fargaba, tana ƙara jawo raguwar zuba jari, amma sun lura cewa kasuwar yanzu na hannun ’yan Najeriya fiye da kasashen waje, don haka ba a sa ran babbar faduwa mai kama da ta 2008. Wasu masana kuma na hasashen kasuwar na iya murmurewa cikin mako mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here