Tinubu Ya Taya Malam Ibrahim Shekarau, Murnar Cika Shekaru 70

0
5

Tinubu Ya Taya Malam Ibrahim Shekarau, Murnar Cika Shekaru 70

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70, a duniya.

Tinubu ya yi yabo ga irin gudunmawar Shekarau a aikin gwamnati, daga malami har ya kai matsayin babban sakatare a Jihar ta Kano kafin ya shiga siyasa a farkon shekarun 2000.

Shugaban ya tunatar da zabin Shekarau a matsayin gwamnan Kano a 2003 da yadda ya mayar da hankali kan jin daɗin al’umma a wa’adin mulkinsa biyu.

Shekarau ya taba rike mukamin Ministan Ilimi (2014-2015) da na Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya (2019-2023).

Tinubu ya gode masa bisa hidimarsa ga ƙasa a matsayin malami, mai gudanarwa, ɗan siyasa, tare da addu’ar Allah ya ba shi lafiya domin ci gaba da hidima ga mutanen sa da Najeriya, kamar yadda Bayo Onanuga, Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Bayanai da Tsare-Tsare, ya sanar.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here