EFCC na neman tsohon ministan man fetur na Najeriya ido rufe
Hukumar EFCC ta bayyana tsohon Ministan Jihar Man Fetur, Timipre Sylva, a matsayin wanda ake nema bisa zargin hada baki da karkatar da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan $14.8.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Litinin, zargin ya shafi wani kudi domin gina matatar mai.
EFCC ta ce an ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema bisa umarnin da wata Kotun Jihar Lagos ta bayar a ranar 6 ga Nuwamba, 2025.
Sanarwar, wacce kakakin EFCC Dele Oyewale ya sa wa hannu, ta bukaci duk wanda ke da sahihin bayani game da inda Sylva yake ya tuntuɓi ofisoshin EFCC a manyan birane ko ya kai rahoto ga rundunar ‘yan sanda ko kowace hukuma ta tsaro.
Hukumar ta kuma bayar da layin waya da adireshin imel domin tura bayanai: 08093322644 da [email protected].


