Burtaniya ta gargaɗi ƴan ƙasar ta akan zuwa Najeriya

0
10

Gwamnatin Birtaniya ta fitar da sabon gargadi ga ’yan ƙasarta kan tafiya Najeriya, tana mai cewa rashin tsaro, garkuwa da mutane, ta’addanci da fashi sun ƙaru a sassan ƙasar.

Burtaniya ta haramta wa ƴa ƴan ta duk wata tafiya zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Katsina da Zamfara saboda barazanar Boko Haram da ISWAP. Haka kuma ƙasar ta ce kar ayi tafiya zuwa Bauchi, Kaduna, Kano, Kebbi, Jigawa, Sokoto, Niger, Kogi, Plateau, Taraba da yankunan wajen Abuja, sai dai in hakan ya zama wajibi.

A yan kwanakin nan dai ana samun ƙaruwar rashin tsaro a wasu sassan kasar nan, musamman a jihohin arewa da wasu sassan kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here