Yau ake gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra

0
10

Kusan mutum miliyan 2.7 a Anambra ne zasu zabi gwamnan jihar a yau Asabar yayin da ake sa ran zaɓen zai fi zafi tsakanin Soludo (APGA), Ukachukwu (APC), Moghalu (LP) da Ezenwafor (PDP).

INEC ta ce kaso 98.8% na masu rijista sun karɓi katin zaɓen su, amma kungiyoyin sa ido kamar Yiaga Africa sun gargaɗi cewa fitowar masu zabe na iya raguwa ƙasa da kaso 20% saboda ƙarancin amincewa da tsarin zabe, musamman tsakanin matasa.

Kungiyoyin farar hula da EU-SDGN sun kuma nuna damuwa kan matsalolin tsaro, yiwuwar amfani da kungiyoyin sa-kai, ƙarancin mata ‘yan takara da yiwuwar jinkirin bude rumfunan zabe. Sai dai ana ganin yanayin tsaro ya fi na zabukan 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here