Mazauna wasu kauyuka a yankunan iyakar Kano da Katsina da ke ƙaramar hukumar Shanono sun fara ficewa daga gidajensu saboda tsananin fargabar hare-haren ƴan bindiga.
Daily Trust ta ruwaito cewa mutane da dama sun koma garin Faruruwa domin neman tsira, yayin da rahotanni ke nuna cewa bayan yarjejeniyar sulhu da aka yi da ƴan bindiga a Katsina, wasu daga cikinsu suna kwarara zuwa kauyukan Kano, inda suke kai farmaki da sace-sacen mutane.
Wani mazaunin yankin Santar Abuja ya ce suna cikin tashin hankali saboda hare-haren na iya faruwa a ko wanne lokaci, lamarin da ya tilasta musu yin hijira zuwa Shanono. Ya bayyana cewa kauyensu yanzu ya zama kufai, inda wasu ke kwana a titi ko gonaki, yayin da iyalinsa mata huɗu da yara 24 suka tsere zuwa wurin wani.
Kauyukan Unguwar Kudu, ’Yan Kwada, Malamai, Santar Abuja, Unguwar Tsamiya, Goron Dutse, Tudun Fulani da Kulki ne lamarin ya fi shafa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da aikin sojoji sannan ya bukace su dasu ƙara ƙoƙari wajen kawar da barazanar tsaro, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ba su dukkan goyon bayan da ake bukata.


