Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ja kunnen ‘yan siyasa da su daina rikitar da batun tsaro saboda bambancin siyasa, yana mai cewa ya kamata a banbance suka ga gwamnati da kuma maganganun da za su cutar da ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da manyan jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS suka kai masa ziyara a gidan Gwamnatin Kaduna. Ya ce wasu ‘yan adawa suna bata sunan ƙasar nan ta hanyar bayyana kalamai a kafafen watsa labarai da ka iya haifar da rikici, yana kiran su “makiyan dimokuradiyya”.
A ƙarshe, ya yaba wa mai taimakawa Shugaban ƙasa a sha’anin tsaro Nuhu Ribadu da shugabannin hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na magance matsalolin tsaro a Najeriya.


