Tsohon mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya dora laifin tabarbarewar tsaro a Najeriya kan jagororin da suka yi mulki a baya da kuma na yanzu.
A wata hira da Arise TV ranar Juma’a, Baba-Ahmed ya ce tsaron Najeriya ya tabarbare ne saboda rashin shugabanci mai nagarta tsawon shekaru 10 zuwa 15 da suka gabata.
“Lamarin ya lalace, tun bayan mutuwar Yar’Adua har zuwa yau,” in ji shi.
Baba-Ahmed ya ce shugabannin baya da na yanzu sun gaza, ciki har da shugabanni biyu da suka gabaci Tinubu, inda ya nuna cewa babu wanda ya yi muhimmiyar nasara wajen magance matsalar tsaro.
Amurka ba za ta gyara Najeriya ba, kuma tsoma bakin ƙasashen waje zai iya raunana ƙasar.


