An farmaki ƴan wasan Barau FC a Katsina

0
10

An sami tashin hankali a ranar Asabar lokacin wasan NPFL tsakanin Katsina United da Barau FC, bayan da wasu magoya bayan Katsina, suka mamaye filin wasa suka kai hari kan ɗan wasan Barau FC, Nana Abraham, wanda ya ji mummunan rauni a wuya.

Lamarin ya faru ne bayan da Orji Kalu na Barau FC ya zura kwallo a minti na 69 ya zama 1-1, wanda ya tayar da hankalin wasu magoya bayan Katsina United. Ƙungiyar Barau FC ta tabbatar da faruwar harin a shafinta na X, tana cewa wasan ya tsaya na ɗan lokaci saboda tashin hankali da ya biyo baya.

Hotunan wurin sun nuna Abraham yana zubar da jini yayin da jami’an tsaro da ’yan wasa ke ƙoƙarin kwantar da tarzoma. Bayan ɗan dakatawar da aka yi, an cigaba da wasan kuma ya kare da ci 1-1.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here