Tinubu zai karɓi rahoton kashe kashen mutane a jihar Filato

0
12
Tinubu
Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shirin karɓar rahoton ƙarshe daga kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken hare-haren da ake ta fama da su a Jihar Filato.

Shugaban kwamitin, Hon. Wale Ahmed, ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai ga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a Abuja. Ya ce kwamitin ya kammala tattaunawa da muhimman bangarori kuma zai miƙa cikakken rahotonsa ga Majalisa da Shugaban Kasa nan bada jimawa ba.

Ahmed ya bayyana cewa rahoton ya dogara ne kan bayanai daga sama da mutane da kungiyoyi 300 da kwamitin ya tattauna da su, ciki har da tsohon Gwamna Joshua Dariye, shugabannin gargajiya, kungiyoyin farar hula, masu ruwa da tsaki, da hukumomin tsaro. Haka kuma kwamitin ya karɓi takardu da bayanai daga masu ruwa da tsaki, ciki har da tsohon kwamandan Operation Safe Haven, Janar Rogers.

Ya ce bayanan da aka tattara sun taimaka wajen gano manyan dalilan rikicin jihar da kuma hanyoyin da za su kawo zaman lafiya mai ɗorewa.

A nasa bangaren, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Yilwatda, ya yaba da matakin Majalisar, yana mai cewa hare-haren sun hallaka mutane da dama tare da durƙusar da tattalin arzikin jihohin Filato. Ya bukaci gwamnati ta hanzarta ɗaukar mataki kan abin da rahoton ya ƙunsa domin dawo da zaman lafiya da farfaɗo da yawon shakatawa da zuba jari a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here