Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a fadar sa da ke Abuja, a yayin da maganganun barazanar hari daga Donald Trump ke ƙara jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar nan.
Ganawar ta zo ne jim kaɗan bayan Tinubu ya tattauna da babban malamin addinin Kirista, Ignatius Kaigama.
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, ana hasashen cewa ganawar na da alaƙa da ƙoƙarin kwantar da hankula, musamman ganin yadda ake yaɗa zargin cewa ana barazanar kisan ƙare-dangi ga mabiya addinin Kirista a Najeriya.
Daga baya, Sarkin Musulmi ya halarci sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa.


