Rasha ta bayyana cewa tana bibiyar rahotannin da ke nuna cewa Amurka na iya ɗaukar matakin soja kan Nijeriya, sakamakon barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa zai kai hari don “kare Kiristoci” a ƙasar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, ta yi wannan bayani a Moscow yayin wani taron manema labarai. Ta bukaci Washington da sauran ɓangarori su mutunta ka’idojin dokokin ƙasa da ƙasa.
Trump, a ranar 1 ga Nuwamba, ya ce ya bai wa Pentagon umarnin fara nazarin yiwuwar daukar matakin soja a Nijeriya. Sai dai kalamansa sun ja hankalin ƙasashen duniya, ciki har da Rasha, wacce ta ce dole a kiyaye ikon kowace ƙasa da ka’idojin duniya.
Gwamnatin Nijeriya ta maida martani cikin wannan makon, inda Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce irin waɗannan kalamai na iya tayar da tarzoma, yana jan hankalin duniya kada ta maimaita abin da ya faru a Sudan.


